Wata kotun majistire a Kano a ranar Alhamis ta bayar da umarnin tsare wasu mutane uku bisa zargin kashe wata matar aure mai suna Fatima Abubakar mai shekaru 35 da kuma ’ya’yanta guda shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano.
Mutanen da ake tuhuma su ne Auwalu mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi, da Yakubu Abdulaziz mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharada.
Ana shari’ar mutanen ne kan tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi haɗa baki, shiga gida ba tare da izini ba, fashi da makami, kisan kai, fyade, ƙona dukiya, mallakar makamai masu haɗari da kuma jikkata mutane.
Mai gabatar da ƙara kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Abdulkarim Maude SAN, ya shaida wa kotu cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 17 ga watan Janairu 2026 a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano.
Maude ya bayyana cewa Umar, wanda yake ɗan uwan matar da aka kashe, ya haɗa baki da sauran mutanen tare da shiga gidan matar ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa, a yayin wannan lamari mutanen sun kashe matar auren tare da ’ya’yanta guda shida.
Haka kuma mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa a baya mutanen sun kai hari, sun yi fashi, sun kashe tare da ƙona wasu mata biyu a unguwar Tudun Yola a watan Nuwamba na shekarar 2025.
Haka zalika, kotun ta bayar da umarnin tsare Umar Ali, wanda ake zargi da karɓar idanuwan wata yarinya ’yar shekara tara, inda aka ce Umar na farko ne ya cire mata idanuwan bayan ya yi mata fyade.
Mutanen da ake tuhuma sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Kotun ta bayyana cewa laifukan sun saɓa wa sashe-sashe na dokar Penal Code da suka haɗa da sashi na 97, 221, 283, 298, 319, 336 da 348.
Lauyan da ke kare mutanen, A. S. Tunkuye, ya gabatar da buƙata bisa sashe na 36(5)(c), inda ya nemi kotu ta umurci Babban Lauyan Jihar ya ba shi damar samun dukkan bayanai da kundin shari’ar domin shirya kariya.
Babban majistire Auwal Yusuf-Suleiman ya bayar da umarnin tsare mutanen a gidan gyaran hali tare da umartar ɓangaren ƙara da su samar wa kariya dukkan abubuwan da suka dace.
Yusuf-Suleiman ya ɗage shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Maris 2026 domin ci gaba da sauraro.
NAN












































