BIDIYO: Harin Jirgin Kasa-Wadanda aka yi garkuwa da su sun magantu

Bidiyon mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya fito ranar Lahadi.

Bidiyon ya nuna yadda masu garkuwa da mutanen suka kewaye su a wani fili mai fadin gaske, suna rokon gwamnati da ta dauki mataki.

Jaaridaar Solacebase ta ruwaito cewa a cikin faifan bidiyo da ya bayyana tun da misalin karfe 2 da mintuna 13, na ranar mai tsawon mintuna biyu da dakika goma sha uku, ya nuna wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun bayyana kansu a matsayin daliban jami’ar jihar Kaduna.

Karanta wannan: Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon hatsaniya a Illorin

Garkuwa, Jirgin, Kasa, Harin, Kaduna, Abuja
BIDIYO: Harin Jirgin Kasa-Wadanda aka sace sun magantu

Haka kuma ta cikin bidiyon an ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta, da wani majinyacin ido da ke kan hanyar zuwa Kaduna domin ayi masa magani da kuma manajan daraktan bankin manoma Alwan Hassan a cikin bidiyon kafin a sake shi.

An ga wasu daga cikin wadanda aka kama suna kira ga gwamnati da ta kai musu dauki.

“Mu ne fasinjojin jirgin kasa da suka taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, na shekarar nan da muke ciki ta 2022, a kan hanyarmu an kai mana hari aka yi garkuwa da mu, kuma tsakanin wancan lokacin zuwa yanzu, mu kadai muka san irin yanayin da muka shiga, akwai mata da yara a cikinmu, akwai tsofaffi da marasa lafiya’’.

“Muna cikin yanayi mara dadi, don haka muna kira ga abokanmu da iyalanmu da gwamnati kan su yi wani abu cikin gaggawa.” Inji guda cikin wadanda abin ya shafa ya fada a cikin faifan bidiyon.

‘Yan ta’addan a wani faifan bidiyo da suka fitar a baya tare da Manajan Daraktan Bankin Manoma, Alwan Hassan ya bayyana cewa sun saki Manajan na bankin ne saboda shekarun sa da kuma watan Ramadan.

Ko da yake majiyar ta shaida wa jaridar Solacebase cewa an karbi sama da Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin a saki Manajan Daraktan.

‘Yan ta’addan da ke cikin bidiyon sun ce ba sa bukatar kudi amma gwamnati ta san bukatarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here