Zargin ta’addanci: Kotu ta bayar da umarnin kama waɗanda ake zargi da alaƙa da Bello Turji

Turji Bello 750x430

Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kama mutane biyar da ake zargi da alaƙa da fitaccen jagoran ta’addanci Bello Turji, bayan sun kasa halartar zaman kotu domin fara shari’ar da ake yi musu.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin bayan lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya gabatar da buƙatar baki a gaban kotu, sakamakon rashin bayyanar waɗanda ake tuhuma a zaman shari’ar.

Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu wanda ake kira Doctor, Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma, inda babu ko guda daga cikinsu da ya halarci kotu a ranar da aka tsara don ci gaba da shari’ar.

Lauyan kare su, A.M. Lukman, ya shaida wa kotu cewa ya tuntuɓi Musa Kamarawa wanda ya tabbatar masa da cewa za su zo kotu, amma ya bayyana mamakinsa kan yadda ba su bayyana ba, lamarin da ya sa kotu ta amince da buƙatar bayar da sammacin kama su.

Mai shari’a Nwite ya dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci na gaba domin ci gaba da Shari’a.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa a baya kotu ta amince da buƙatar gwamnatin tarayya na sake buɗe tuhumar ta’addanci da aka shigar a kansu, bayan an taɓa soke ta saboda rashin himma wajen gurfanar da shari’ar.

Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume masu yawa kan waɗanda ake zargin da kuma wasu da ke gudun hijira ciki har da Bello Turji, inda ake zargin su da tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta hanyar samar da kwayoyi, abinci, kayan sojoji da ‘yan sanda, da kayan gini zuwa sansanonin ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara, Sakkwato da Kaduna.

Ana kuma zargin wasu daga cikinsu da taimakawa sayen manyan motocin yaƙi da bayar da kulawar jinya ga Bello Turji bayan harin da ya jagoranta a wani ƙauye a Jihar Zamfara, laifukan da suka saba wa dokar hana ta’addanci ta ƙasa, kuma kotu ta bayyana cewa shari’ar za ta ci gaba da zarar an kama waɗanda ake nema.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here