Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bukaci babbar kotun birnin tarayya Abuja da ta hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa kira karin shedu bayan wasu 10 da suka ba da shaida a shari’ar sa da ake yi ta zamba.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa (SAN), ya ce tun da EFCC ta lissafa shaidu 10 kacal a cikin shaidun da ta shigar a kotu, bai kamata a bari ta kara wasu shaidu ba.
Sai dai lauya mai shigar da kara na EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya ki amincewa da bukatar, yana mai cewa ya zama dole a kara bayar da shaida domin a tabbatar da adalci kan gabatar da karar.
Oyedepo ya bayar da hujjar cewa hana hukumar damar kiran karin shedu zai tauye hakkinsu na sauraron karar.
Labari mai alaƙa: Zamba a Intanet: EFCC ta kama wasu ‘yan kasar China 4, da wasu karin mutane 101
Bayan samun gardama daga bangarori daban-daban a ranar Litinin, Mai shari’a Hamza Muazu ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga Maris domin yanke hukunci.
Emefiele yana fuskantar tuhume-tuhume guda 20, wadanda ke da alaka da laifin cin amana.
An kuma zarge shi da yin amfani da mukaminsa na gwamnan babban bankin kasa CBN wajen bayar da cin hanci da rashawa ga kamfanoni guda biyu.