Ƴan sanda sun kama wani ɗan jaridar nan mai zaman kansa daga Kano mai suna Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano a ranar Asabar.
Kamen nasa ya biyo bayan ƙorafi da aka shigar a kansa bisa zargin alaƙanta Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar mai kula da shige da ficen Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama shi ne bisa zargin ɓata suna.
Solacebase ta ruwaito cewa jami’an ’yan sanda daga hedkwatar shiyyar Zone 1 ne suka kama Dan’uwa Rano a ofishinsa da ke cikin birnin Kano ba tare da nuna masa takardar kame ba.
Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa hukumomin yaƙi da cin hanci irin su hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da kuma hukumar EFCC sun gano sama da naira biliyan 6.5 da ake zargin an danganta da Abdullahi Rogo, wanda ke kula da sashen hulɗa da baki a gidan gwamnati na Kano.
A cewar takardun kotu, an ce Abdullahi Rogo ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati ta hannun wasu kamfanoni kamar H&M Nigeria Limited, A.Y. Maikifi Petroleum, da Ammas Oil and Gas Limited don yin kwangiloli ta ƙarya.
Bincike ya nuna cewa an biya kuɗaɗen da ake magana a kai ba tare da an gudanar da ayyukan da aka ce an ba da su ba.
Rahotanni sun ƙara bayyana cewa ICPC ta karɓo sama da naira biliyan 1.1 daga kamfanonin da abin ya shafa, kuma kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin karɓe ragowar naira miliyan 142.2 da ke cikin asusun Rogo.
Haka kuma, asusun kamfanin Rogo da ke bankin Alternative Bank ya karɓi shigar kuɗi sama da biliyan 3 da kuma fitar kuɗi kusan biliyan 2.5 tsakanin watan Agusta 2024 da Fabrairu 2025.
Duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin yaki da cin hanci a gwamnatinsa, bincike ya gano cewa har asusun sirrin Rogo da ke bankin Zenith ya karɓi sama da naira biliyan 2.2 a cikin shekaru uku.
Rahoton yace Rogo ya amsa laifi a gaban hukumar ICPC, sai dai daga baya ya kai ƙara kotun jihar Kano domin hana cafkarsa da gurfanar da shi.
Dan’uwa Rano ya tabbatarwa solacebase cewa ƙorafin da aka shigar a kansa na da nasaba da wani shirin siyasa a tasharsa ta YouTube mai suna Imalu, wanda Rogo ke zargin ya bata masa suna.
Sai dai ’yan sanda na kuma bincikar Ɗan uwa bisa zargin gudanar da aikin jarida ba tare da lasisin hukumar sadarwa ta ƙasa (NBC) ba.
Rahotanni sun nuna cewa ana iya tsare shi har zuwa Litinin domin gabatar da shi gaban kotu.













































