Zargin ɓatanci ga Annabi: Majalisar Shura ta Kano ta gayyaci Sheikh Lawan Triumph da masu ƙorafi

WhatsApp Image 2025 09 27 at 00.17.15 750x430

Majalisar Shura ta Jihar Kano ta yanke shawarar gayyatar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Triumph, tare da masu ƙorafi domin yi musu tambayoyi kan zargin yin kalaman cin mutunci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da aka yi masa.

Sakataren majalisar, Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a ranar Juma’a, bayan kammala taron majalisar.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin Kano ta aika ƙorafe-ƙorafe kan Sheikh Lawan Triumph zuwa Majalisar Shura

Ya ce kwamitin da Wadiyan Colonel ke jagoranta ya yanke shawarar cewa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa za a kira su domin su gabatar da hujjoji da kuma kare kansu.

Rahotanni sun nuna cewa cece-kuce ya barke ne bayan wasu mutane suka kai ƙara kan cewa Sheikh Triumph ya yi wasu maganganu masu ɓata suna ga Annabi, ciki har da cewa Annabin ya taɓa yin fitsari tsaye, cewa ba wani abin al’ajabi a haihuwarsa, da kuma cewa iyayensa suna cikin wuta.

Lamarin ya ja hankalin jama’a tare da haddasa muhawara a fili, inda ake nuna damuwa kan yiwuwar tayar da tarzoma a Kano.

Bisa haka ne gwamnatin jihar ta mika batun ga Majalisar Shura, wacce ta ƙunshi manyan malamai domin duba al’amarin bisa ga shari’ar Musulunci.

Majalisar ta bayyana cewa manufarta ita ce ta tabbatar da bin doka da lumana wajen warware lamarin, tare da bayar da shawarwari bisa ga shari’ar addini.

Sagagi ya yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali da kuma kiyaye zaman lafiya, yana mai jaddada muhimmancin kwanciyar hankali wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na jihar.

Ya ce, “Kwamitin zai binciki zargin da kyau, sannan zai ba gwamnati shawara bisa ga shari’ar Musulunci.

Malamin da kuma masu ƙorafi za a ba su dama ɗaya wajen gabatar da hujjoji da kare kansu.”

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here