Zargin Ɓatanci: Abduljabbar Ya yi Rashin Nasara a Kotun Tarayya

120582890 bbcabduljabbar
120582890 bbcabduljabbar

Koton tarayya dake zamanta a Abuja a yau Litinin, tayi watsi da karar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar gabanta yana kalubalantar Gwamnatin Kano kan take hakki bisa shari’ar da ake yi masa kan zargin kalaman batanci.

Mai shari’a Emeka Nwite, a yayin yanke hukuncin, ya kori karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan cewa cin zarafin kotu ne, kasancewar an shigar da irin karar a gaban kotun tarayya dake zamanta a Kano.

Mai shari’ar yayi Allah wadai da yunkurin lauyan Abduljabbar wato Shehu Dalhatu na shigar da irin karar da ya kai ga kotun ta Kano.

Jaridar solacebase ta rawaito cewa Abduljabbar Kabara ta hannun lauyansa, Dalhatu Shehu ya kai karar Kotun shari’a dake zamanta a Kofar Kudu da gwamnatin jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here