Zargin ɓatanci a shafin sada zumunta: Kotu za ta saurari tuhumar raina umarnin kotu da Sanata Akpoti-Udughan ta yi

Senator Natasha Akpoti Uduaghan and Akpabio 750x430

Babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta ci gaba da sauraren tuhumar cin mutunci da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shigar a kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, kan zargin wani sako da ta wallafa a dandalin sada zumunta wanda ya saba wa umarnin kotu.

Mai shari’a Binta Nyako, wadda ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Talata da karfe 12 na rana, ta kuma ce za ta ci gaba da sauraren tuhumar rashin bin umarnin kotu da Akpoti-Uduaghan ta yi a baya kan Akpabio da Majalisar Dattawa da sauran su kan zargin kin bin umarnin kotu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Mai shari’a Nyako, a ranar 4 ga watan Afrilu, ta haramtawa duk wanda ke cikin karar da Akpoti-Udughan ta shigar a gaban kotu daga yin hira da kafafen yada labarai ko kuma shiga shafukan sada zumunta dangane da batun da ke gaban kotu.

Wannan mataki ya biyo bayan korafin da lauyan Akpabio, Kehinde Ogunwumiju, SAN, ya yi, na cewa Akpoti-Uduaghan na tafiya daga wata kafar yada labarai zuwa wani, inda ta yi hira da manema labarai kan batutuwan da suka shafi karar.

Sai dai Akpabio ya shigar da karar ne inda ya zarge ta da kin bin umarnin kotu ta hanyar sanya wata “wasika mai dauki da habaici” a shafinta na Facebook.

Har ila yau, Akpoti-Uduaghan ta shigar da kara a gaban kotu bisa zargin Akpabio da dakatar da ita wanda ya sabawa umarnin da tsohon alkalin kotun, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar, na hana duk wadanda ake kara daukar wani mataki har sai an saurari shari’ar da kuma yanke hukunci. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here