Zan taya Tinubu yaƙin neman zaɓe — Buhari 

Screenshot 20221222 100708
Screenshot 20221222 100708

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa jam’iyyar APC, da ƴan takararta tabbacin cewa zai tabbatar da nasarar zaben shugaban kasa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

A cewarsa, a shirye yake a kowane lokaci don yin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa da kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyar da “cikakken kuzari da tabbaci.”

Shugaban ya bayyana cewa an ba da wannan tabbacin ne domin kawar da damuwar da wasu ke nuna cewa bai fito a yakin neman zabe ba tun bayan kaddamar da shi a Jos, jihar Plateau.

Sai dai ya jaddada cewa duk da yake ya jajirce kan siyasa, ayyukan shugaban kasa za su ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Shehu ya tuna cewa shugaban kasar a lokacin da yake zantawa da al’ummar Najeriya a birnin Washington DC a ziyarar da ya kai kasar Amurka a kwanakin baya, ya jaddada abin da ya fada a duk lokacin da ya ke cewa a shirye yake ya yi kamfen din ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaben shekara mai zuwa.

Shugaban ya ce ya zuwa yanzu yakin neman zaben APC ya kasance mafi karfi a tarihi.

Mista Buhari ya bayyana kwarin guiwar cewa jam’iyyar za ta lashe dukkan zabukan cikin adalci da gaskiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here