“Zan riƙa samun sama da dala miliyan dubu 30 nan da ƙarshen 2024” – Ɗangote

Ɗangote, riƙa, samun, dala, miliyan, dubu, ƙarshen
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, kuma mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa zuwa ƙarshen shekarar nan ta 2024, yana sa...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, kuma mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa zuwa ƙarshen shekarar nan ta 2024, yana sa ran jimillar kuɗin da zai riƙa samu a harkokin kasuwancinsa ya kai sama da dala miliyan dubu 30.

A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta CNN, hamshaƙin attajirin ya ce cimma wannan buri zai sa kuma kamfanin ya kasance ɗaya daga cikin manya-manyan kamfanoni 120 na duniya.

Karin labari: Rundunar Sojojin Najeriya ta karyata kewaye gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago yayin zaman tattaunawa

Attajirin ya ce, yadda ya sauya fasalin kamfanin ta yadda manyan jami’ai ke jagorantar muhimman ɓangarori na harkokin kasuwancin nasa, cimma wannan buri na samun dala biliyan 30 zuwa ƙarshen shekarar ba abu ne da zai zama mai wahala ba.

“Mun raba kamfanin gida biyu a yanzu. Ni ina matsayin shugaban rukunin, sannan kuma akwai shugabannin rukunin na ɓangaren mai da iskar gas, sai kuma shugaban rukunin sauran harkokin kasuwancin,” in ji shi.

Karin labari: Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta gayyaci ma’aikata kan yajin aikin mafi karancin albashi

Ya ƙara da cewa, ”duka waɗannan idan ka haɗa su, zuwa ƙarshen shekarar nan, za mu samu rukunin kamafanin da zai samu dala biliyan 30, kuma wannan babban abu ne.

“Hakan na nufin za mu kasance cikin manyan kamfanonin duniya 120.” kamar yadda jaridar BBC Hausa ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here