Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Esther Dawaki da Shehu Aliyu Fatange a gaban kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin hada baki da yin wadaƙa da kudi da kuma sayen kuri’u da ya kai naira miliyan 26.
A cewar mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, an kama wadanda ake tuhumar a ranar 16 ga Agusta, 2025 a Kaduna, tare da kudi Naira Miliyan 26,463,000 da ake zargin an ware su domin amfani da su wajen sayen kuri’u a zaben cike gurbi na mazabar Chikun/Kajuru.
An gano kudin ne a cikin motar Toyota Corolla mallakin Fatange, wadda aka ajiye a cikin otal a Kaduna.
Karin labari: Mele Kyari ya bar ofishin EFCC bayan amsa tambayoyi
Fatange ya bayyana kansa a matsayin daraktan janar na kamfen din dan takarar jam’iyyar PDP a zaben.
Daya daga cikin tuhume-tuhumen na cewa Dawaki ya sa Fatange ya karbi kudi sama da Naira Miliyan 26 ba tare da ya bi ta hanyar cibiyar kudi ba, wanda ya saba wa doka.
Dukkan wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifi a gaban kotu. Lauyan EFCC, O. O. Arumemi, ya nemi a dage shari’ar tare da neman a tura su gidan gyaran hali.
Sai dai lauyoyin kare su, E. N. Ogbu da A. A. Ashat, sun bukaci a bar su a hannun EFCC har sai an yanke hukunci kan bukatar belinsu.
Alkalin kotun, Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a tura Dawaki zuwa gidan gyaran hali na Suleja, yayin da aka tura Fatange zuwa na Kuje.
An dage shari’ar zuwa 15 ga Satumba domin sauraron bukatar belin su













































