Zaben ƙananan hukumomi: Hukumar zabe ta Osun ta raba shaidar cin zabe ga sabbin shugabanni

Osun LG Chairmen1

Zababbun shugabannin kananan hukumomi 30 na jihar Osun sun karbi takardar shaidar cin zabe.

A ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ta lashe dukkan kananan hukumomi 30 na shugaban ƙaramar hukuma da kansiloli a jihar da ke Kudu-maso-Yamma, inda kwana daya bayan haka hukumar ta gabatar da shaidar cin zabe ga shugabannin.

Jami’ar yada labarai ta Hukumar, Sadiat Isiaka, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.

Karin karatu: Da ɗumi-ɗumi: PDP ta lashe dukkanin kananan hukumomi 30 a jihar Osun

Ta ce Shugaban OSIEC, Barista Hashim Abioye, ya taya zababbun shugabannin murnar nasarar da suka samu, ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari ga dimokuradiyya ta fuskar da’a da kuma yi wa jama’a hidima.

Jam’iyyar PDP reshen jihar ta yabawa zababbun ‘yan takarar da suka yi amfani da ‘yancinsu na dimokradiyya a zaben kananan hukumomin da aka yi ranar Asabar.

Shugaban jam’iyyar na jihar Osun, Hon. Sunday Bisi, ya bayyana masu kada kuri’a a matsayin jaruman dimokradiyya.

Bisi ya kuma yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan da suka faru kwanaki kafin zaben, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kama wani Ademoti Adeboye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here