Za mu binciki ƙaramar hukumar Tudunwada- Majalisar Dokokin Kano

Polish 20250717 130106943

Biyo bayan ƙofarin wasu manoma ƴan asalin ƙaramar hukumar Tudunwada, Majalisar dokokin Kano, ta ce, za ta gudanar da bincike bisa zargin shugabancin Ƙaramar Hukumar karkashin jagorancin Hajiya Hajiya Sa’adatu Yusha’u, kan ƙwace WA  mutanen gonakinsu da ke Dajin Gurfa.

‎Freedom Radio ta ruwaito cewa, shugaban masu rinjaye na zauren Majalisar Lawan Hussain Cediyar ƴan Gurasa ne ya bayyana haka lokacin ganawarsa da ƙungiyar kare hakkin Ɗan-adam da tabbatar da daidaito a cikin al’umma wadda ta kai wa Majalisar ƙorafin Manoman.

Shugaban ƙungiyar Malam Sa’id Bin Usman, ya ce, akwai ƙorafi mai yawa kan matsalolin hakkin mallakar gonaki tsakanin shugabancin Ƙaramar Hukumar ta Tudunwada da kuma manoman yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here