Za mu bijire wa shirin ƙara kuɗin man fetur a Najeriya – ‘Yan fafutuka

1688201112710
1688201112710

Wata gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ranar Juma’a ta ce za ta bijire wa shirin ƙara farashin man fetur da ake zargin ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya (IPMAN) na ƙoƙarin yi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato wata sanarwa da haɗin gwiwar, Dr Basil Musa da Mallam Haruna Maigida suka fitar na cewa za su bijirewa yunƙurin IPMAN, na ƙara farashin litar man fetur zuwa N700 ta hanyar rufe gidajen man IPMAN da ke faɗin Najeriya.

Ƙungiyoyin dai sun haɗar da Oil and Gas Transparency and Advocacy Group da Civil Society Coalition for Economic Development (CED), da Centre for Citizens Rights da Centre for Good Governance Advocacy da kuma Action against Corruption in Nigeria, da sauransu.

Sun dai zargi IPMAN da zama kishiyar gwamnati da ƙara tsanani a kan talakawan Najeriya, ta hanyar ƙarin farashin man fetur su kaɗai.

Gamayyar ƙungiyoyin ya ce shirin ƙara farashin man abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da IPMAN daga abin da ta yi zargin cewa ci da gumin talakawan Najeriya ne.

Sun kuma ce matakin wani zagon ƙasa ne ga tattalin arziƙin ƙasar don kuwa ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga halin gigitar da suka shiga bayan ƙara farashin man fetur na ranar 29 ga watan Mayu.

‘Yan Najeriya da ma suna cikin mawuyacin hali in ji su, saboda ƙarin kuɗin man fetur na baya-bayan nan ba tare da ɓullo da matakan rage raɗaɗi ba.

Sun dai lashi takobin gangamo wakilansu da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin jihohin ƙasar 36 don gudanar da zanga-zanga, kuma a cewarsu zanga-zangar za ta mayar da hankali wajen garƙame gidajen mai a fadin Najeriya.

A baya-bayan nan dai, wani jami’in IPMAN Bashir Ɗan Mallam ya shaida wa BBC cewa matakin nasu ya ta’allaƙa ne a kan farashin dalar Amurka, wanda idan ana samun dala cikin sauƙi farashin man fetur zai yi ƙasa, idan kuma dala ta yi wahala, ba shakka farashin mai zai tashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here