Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya ce, nan ba da dadewa ba za a fara ayyukan layin dogo masu amfani da Lantarki a jihohin Arewacin Najeriya.
Alkali, ya bayyana hakan ne a wajen taron samar da ababen more rayuwa a gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation da ake gudanar da taron kwana biyu kan hada-hadar gwamnati da jama’a a ranar Laraba a Kaduna.
A cewarsa, aikin wanda za a fara shi da Kaduna da Kano, wani bangare ne na kokarin inganta sufurin jama’a da bunkasa tattalin arziki da ci gaban yankin.
“Za a gudanar da wannan aikin ne ta hanyar ma’aikatar Kudi a tsarin Incorporated MOFI,” in ji shi.
Akan aikin sabuntawa da kara inganta rayuwar al’umma watau Renewed Hope Cities Project, Alkali ya bayyana cewa, an kammala gina gidaje a guda 3,112 a babban birnin tarayya Abuja.
Ya kuma ce, Kano na da gidaje 1,500 da kuma karin gidaje 500 a karkashin wannan aikin.
Alkali ya kuma kara da cewa, ana shirin samar da gidaje guda 250 a kowacce jiha, yayin da a jihohin Sokoto da Gombe da Yobe da Katsina da Nasarawa da Benue kuma aka kammala su.
“Ayyukan za su samar da ayyukan yi sama da 250,000 a wurare daban-daban, inda ma’aikata ke samun matsakaicin albashi na Naira 150,000 duk wata.
“Za kuma su kara kaimi wajen samar da cibiyoyin gine-gine tare da jawo jarin sama da biliyan 70 na kamfanoni masu zaman kansu.
“Akan aikin gyaran hanyar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano, an kammala kashi 53 cikin 100.
“Haka zalika aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi an kammala shi da kaso 61 cikin 100.
“Bugu da kari, an kammala wani bangare na Port Harcourt zuwa Maiduguri an samu nasarar kammala tsawon kilomita 61 inda aka fara yin amfani da shi,” inji Alkali.













































