Tsoffin shugabannin kananan hukumomin jihar Kano da suka yi aiki tsakanin 2019 zuwa 2022 sun bayyana goyon bayansu ga mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Barau I. Jibrin, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC kaɗai a zaben gwamnan jihar Kano na 2027.
Tsoffin shugabannin sun ɗauki wannan mataki ne a lokacin da suka kai ziyarar ban girma majalisar dokoki ta tarayya a Abuja, inda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, Barrista Dahiru Mannir Maigari, ya gabatar da matakin goyon bayansu, sannan tsohon shugaban ƙungiyar ALGON na jihar, Baffa Mohammed Takai, ya mara masa baya.
Daga nan aka kada kuri’ar murya wadda dukkan tsoffin shugabannin suka amince da ita gaba ɗaya, a gaban mambobin majalisar dokokin jihar Kano biyu da suka halarta domin shaida taron.
A wata sanarwa daga mai bai wa mataimakin shugaban majalisar dattijai shawara kan yaɗa labarai, Ismail Mudashir ya fitar , ta ce tsoffin shugabannin kananan hukumomin sun bukaci Sanata Barau ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamna cikin gaggawa.
Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Khalid Ishak Diso, ya yi nuni da cewa jama’ar jihar Kano suna sa ran ganin Barau ya amsa kiran da ake yi masa na ya tsaya takarar gwamna, kasancewarsa ɗan siyasar da ke da alaƙa da talakawa.
Takai, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce sun ɗauki Sanata Barau ne saboda bajintarsa a majalisar dattijai da irin rawar da yake takawa wajen cigaban jihar Kano.
A nasa ɓangaren, Sanata Barau ya gode musu bisa goyon baya, tare da cewa jihar Kano ta ja baya idan aka kwatanta da shekarub baya sakamakon rashin kyakkyawan jagoranci, don haka akwai bukatar haɗa kai wajen dawo da martabar jihar.
A wani bangare kuma, wakilai daga kananan hukumomin Tsanyawa da Ghari sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Barau a wata ziyara daban da suka kai masa, inda mambobin majalisar dokokin jihar suka jagoranci matakin amincewa, tare da samun goyon bayan jama’a sama da 100 da suka halarta.
Sun tabbatar masa cewa al’ummarsu na goyon bayansa gaba ɗaya, yayin da shi kuma ya tabbatar musu da cewa an ɗauki matakai wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu.













































