Jam’iyyar APC ta ayyana zaben fitar da gwani na gwamna a jihar Edo a matsayin wanda bai kammala ba.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa Felix Morka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata domin bayyana matsayar jam’iyyar kan zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Jam’iyyar mai mulki ta ce za’a gudanar da wani sabon zaɓen a ranar Alhamis domin tantance wanda zai tsaya mata takarar gwamna a jihar a watan Satumbar 2024.
Karin labari: Akpabio ya fallasa gwamnoni da karbar Naira Biliyan 30
Jam’iyyar ta kira taron gaggawa na kwamitin ayyuka na kasa a daren ranar Talata domin warware rikicin da ya kunno kai a zaben fidda gwani da kwamitin Sanata Hope Uzodimma ya jagoranta.
Morka ya ce, “a taron gaggawar da jam’iyyar tayi na ranar Talata, 20 ga watan Faburairu 2024 domin duba kan batun zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Edo, kwamitin gudanarwa ta tattauna batun sannan ta yanke shawarar cewa zaɓen bai kammala ba sannan ta tsaida ranar Alhamis 22 ga watan Faburairu a matsayin ranar kammala zaɓen fidda gwanin a jihar.”
Karin labari: Majalisar dattawa za ta binciki Emefiele da tsohuwar gwamnatin Buhari
Hatsaniya ta biyo bayan zaben fitar da gwanin da aka gudanar yayin da wasu ƴan takara biyu su ka yi ikirarin cewa su ne suke da tikitin tsayawa takara a jam’iyyar bayan da shugaban kwamitin shirya zaɓen Uzodinma ya ayyana Dennis Idahosa a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Jami’in zaɓen Stanley Ugboaja daga baya ya fito ya ayyana Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen duk da Anamero Dekeri yayi ikirarin shi ne ke da tikitin.
Karin labari: MDD ta ware dala miliyan 100 don ayyukan jinkai a kasashe 7
Uku daga cin ƴan takara sha biyu da aka zaɓa domin tsayawa takarar zaɓen fidda gwanin sun janye kafin lokacin. Sun haɗa da Osagie Ize-Iyamu da Lucky Imasuen da kuma Ernest Umakhihe.
‘Ƴan takarar da ba su gamsu da sakamakon zaɓen ba sun yi zanga-zanga a babban offishin jam’iyyar na kasa da ke Abuja.