Zaɓen fidda gwani a Osun: APC ta hana Omisore da wasu shida tsayawa takarar gwamna

Iyiola Omisore 750x430

Jam’iyyar APC a jihar Osun tn hana tsohon sakataren jam’iyyar APC, Sanata Iyiola Omisore, tare da wasu ’yan takara shida shiga zaben fidda gwanin gwamna da jam’iyyar ke shirin gudanarwa a shekarar 2026 a jihar.

Sauran ’yan takarar da aka hana shiga zaben fidda gwanin da aka tsara a ranar 13 ga Disamba sun haɗa da Babatunde Haketer Oralusi, Oyedotun Babayemi, Dr. Akin Ogunbiyi, Benedict Alabi, Adegoke Rasheed Okiki da Sanata Babajide Omoworare.

Wannan matakin ya fito ne daga rahoton da kwamitin tantance ’yan takara, ƙarƙashin jagorancin Chief Obinna Uzoh, ya mikawa kwamitin gudanarwa na ƙasa na APC a Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa akwai kura-kurai da matsaloli a cikin takardun neman tsayawa takara na Omisore da sauran wadanda aka hana shiga zaben fidda gwanin.

APC ta kuma bayyana cewa ba su gabatar da hujjar samun goyon bayan akalla mambobi biyar da suka yi rajista kuma suke biyan kuɗin shekara daga kowace ƙaramar hukuma ta jihar Osun, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ka’idojin ta suka tanada.

A gefe guda kuma, kwamitin ya amince da Mulikat Abiola Jimoh da Munirudeen Bola Oyebamiji domin su ci gaba da shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here