Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta zabi likitan ƙwaƙwalwa a asibitin koyarwa na Jami’ar Jos Farfesa Chris Piwuna a matsayin shugaban kungiyar na gaba.
Piwuna, wanda kuma shi ne shugaban kula da harkokin dalibai a jami’ar Jos, ya karbi mukamin ne daga hannun Victor Osodeke, Farfesa a fannin kimiyyar kasa daga jami’ar noma ta Michael Okpara da ke Umudike a jihar Abia.
An dauki matakin ne a taron wakilan kungiyar na kasa karo na 23, wanda ya gudana a Benin ranar Lahadi.
Zaben dai ya gudana ne tsakanin Piwuna da Farfesa Adamu Babayo daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, kamar yadda majiya mai tushe ta tabbatar da hakan.
Har ila yau, wata majiya ta shaida wa SolaceBase cewa kafin zaben, Farfesa Chris Piwuna, shi ne mataimakin shugaban kungiyar.
Ya ce an kammala zaben ne da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar Litinin.
Karin bayani na nan tafe…













































