YANZU-YANZU: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Bashir Tofa ya rasu

Alhaji Bashir Tofa
Alhaji Bashir Tofa

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar NRC, Alhaji Bashir Tofa ya rasu.

Wata majiya da ga iyalan mamacin ta ce ya rasu ne da asubar yau Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a makon da ya gabata ne dai a ka fara raɗe-raɗin cewa Tofa ya rasu, in da dangin sa su ka tabbatar da cewa bai rasu ba, amma bashi da lafiya.

Marigayin ya rasu yana da shekara 74 bayan da a ka haife shi a ranar 4 ga watan Yuni, a shekarar 1947.

Ƙarin bayani na nan tafe….

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here