Yanzu-yanzu: Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya naɗa Christopher Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya

52aebbcf 588b 406b 8402 a90c53b66e1d.jpg

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sunan Janar Christopher Gwabin Musa ga Majalisar Dattawa domin ta amince da naɗa shi a matsayin sabon ministan tsaron ƙasa.

Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin da tsohon minista, Badaru Abubakar ya yi a ranar Litinin, wanda hakan ya bar gurbin da ake buƙatar cike wa cikin gaggawa.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken tabbacin sa kan ƙwarewar Janar Musa, yana mai cewa zai iya jagorantar ma’aikatar tsaro tare da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

Janar Musa, wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya shafe lokaci mai tsawo yana gudanar da manyan muƙamai a rundunar sojin Najeriya tun bayan kammala karatunsa a NDA a shekarar 1991.

Majalisar Dattawa na sa ran fara duba tabbatar da nadin nasa a makonni masu zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here