Yanzu-yanzu: Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin rundunonin tsaro

Tinubu Tinubu sign 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gudanar da sauye-sauye a manyan muƙaman rundunonin tsaro na ƙasar nan domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

Shugaban ya nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon hafsan hafsoshin tsaro, inda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.

Haka kuma, Manjo Janar W. Shaibu shi ne sabon hafsan sojojin ƙasa, Air Vice Marshall S.K Aneke ya zama hafsan sojojin sama, yayin da Rear Admiral I. Abbas ya karɓi matsayin hafsan rundunar sojojin ruwa.

Janar E.A.P Undiendeye ya ci gaba da zama hafsan leƙen asirin tsaro na ƙasa kamar yadda yake a baya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana godiya ga tsofaffin shugabannin rundunonin tsaro bisa jajircewarsu da sadaukar da kai wajen kare ƙasar.

Shugaba Tinubu ya umurci sabbin shugabannin da su tabbatar sun nuna kwarewa, jajircewa da haɗin kai domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Nadin sabbin shugabannin rundunonin tsaron ya fara aiki nan take.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here