Majalisar dokoki ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke zaune a rukunin ɗakuna mai lamba Suite 2.05 na ɓangaren majalisar dattawa.
An buɗe ofishin ne a ranar Talata ta hannun Mataimakin Daraktan Ma’aikatan Tsaron Majalisar, Alabi Adedeji, abin da zai iya bai wa Sanata mai wakiltar Tsakiyar Jihar Kogi damar komawa zauren majalisar dattawa idan zaman majalisa ya ci gaba a ranar 7 ga watan Oktoba, 2025, a cewar gidan talabijin na tashar Channels.
Wannan ci gaban ya nuna cewa Majalisar ta ba wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar, damar shiga ofishinta da kuma shiga harabar majalisar.
Yanzu da aka buɗe ofishinta, Akpoti-Uduaghan za ta iya shiga harabar majalisar, abin da zai iya bai wa damarta ta ci gaba da aikinta na majalisar dokoki.
An tattaro cewa dalilin buɗe ofishinta kafin a ci gaba da zaman majalisar shi ne domin ba ta damar kasancewa a babban ɗakin majalisar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2025.
A makon da ya gabata, ta rubuta wasiƙa zuwa ga majalisar dattawa domin sanar da su cewa tana son komawa bakin aiki bayan dakatarwarta ta tsawon watanni shida.
Karin bayani zai biyo baya…
NAN













































