Rundunar ‘yan sandan ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, domin yin bincike kan wani lamari da ya faru a yayin bikin Sallah.
SolaceBase ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani Usman Sagiru, mai shekaru 20, mai suna Sharifai Quarters, bisa zargin kisan kai ga wani banga a tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi II bayan sallar idi.
Hakazalika rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin tare da mika goron gayyata ga Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin yi masa tambayoyi.
A cewar wata wasika a hukumance da SolaceBase ta gani mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda ya ce an yi gayyatar ne a karkashin umarnin babban sufeton ‘yan sanda.
Karin karatu: Hotuna: Yadda aka gudanar da Sallar Idi a fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa
Wasikar ta bukaci Sarkin da ya ziyarci hedikwatar hukumar leken asiri da ke Abuja a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025, da karfe 10:00 na safe.
Idan za a iya tunawa Hukumomin tsaro sun sanya takunkumi kan hawan sallah saboda matsalolin tsaro da kuma yiwuwar tashin hankali.
Duk da haka, an yi zargin cewa Sarki Muhammadu Sanusi ya ci gaba da gudanar da hawan inda ya jawo hankulan jama’a da dama da kafafen yada labarai a ranar Sallah da Hawan Nasarawa tare da ziyartar gidan gwamnati.