‘Yan takarar Senegal sun yi kira da a kaɗa kuri’a cikin makonni 6

'Yan takarar, Senegal, kuri'a
'Yan takara 15 daga cikin 20 da aka amince su tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Senegal da aka ɗaga sun buƙaci da a gudanar da sabuwar kuri'ar nan da ranar...

‘Yan takara 15 daga cikin 20 da aka amince su tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Senegal da aka ɗaga sun buƙaci da a gudanar da sabuwar kuri’ar nan da ranar 2 ga watan Afrilu, ranar da shugaba Macky Sall na yanzu zai kawo karshen wa’adinsa.

‘Yan takara 15 kuma sun dage da cewa bai kamata a sauya jerin sunayen ba.

Takardar ta samu sa hannun wasu daga cikin manyan ‘yan takarar da suka hada da Bassirou Diomaye Faye da ake tsare da shi bisa zargin tayar da hargitsi da kuma tsohon magajin garin Dakar Khalifa Sall, wanda ba shi da alaƙa da shugaban ƙasar.

Karanta wannan: Jami’ar Ilọrin UNILORIN ta kori dalibai 9

Shugaba Sall ya so ɗage zaɓen na wasu watanni domin a iya warware takaddamar cancantar wasu ‘yan takara.

Sai dai babbar kotun ƙasar ta ce ɗagewar ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar kuma Mista Sall ya ce a yanzu za’a gudanar da zaben da wuri-wuri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here