Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Abuja

Protesters tear gas 750x430

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Litinin ta tarwatsa masu zanga-zanga da hayaki mai sa hawaye a unguwar Maitama da ke Abuja.

Masu zanga-zangar, wadanda suka taru cikin lumana don bayyana kokensu, sun fada cikin rudani, yayin da jami’an tsaro suka jefa hayaƙi mai sa hawaye ta yadda kowa ke neman tsira da rayuwarsa.

Zanga-zangar wadda wani bangare ne na zanga-zangar da aka yi a fadin kasar nan karkashin jagorancin kungiyar Take-Back da sauran kungiyoyin farar hula, domin jawo hankulan mahukunta kan al’amuran kasa da dama.

Babban abin da ke masu zanga-zangar. Ke nuna damuwa a kai sun hada da zargin yin amfani da dokar ta’addanci ta internet, da tabarbarewar tattalin arziki a kasa, da kuma abin da suka bayyana a matsayin dokar ta-baci a jihar Ribas.

Masu zanga-zangar dai na dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar su “Dakatar da Zalunci” a yayin da suke zagayawa a kan titunan Babban Birnin Tarayya.

Shi ma dan rajin kare hakkin bil adama kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore ya halarci wurin zanga-zangar domin nuna goyon baya ga kungiyar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, jami’in kungiyar Juwon Sanyaolu, ya ce zanga-zangar na da nufin yin tir da abin da ya kira “mulkin kama karya” na gwamnati mai ci da kuma neman agajin gaggawa ga ‘yan Najeriya da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here