’Yan sanda sun fara ƙoƙarin ceto mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi bayan sace shi

Speaker of the Kebbi State House of Assembly Samaila Bagudu

Rundunar ’yan sanda ta jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Samaila Bagudu, da ake zargin ’yan bindiga masu ɗauke da makamai sun sace shi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, babban sufeto Nafiu Abubakar, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, da ƙarfe takwas da mintuna ashirin na dare.

Sanarwar ta ce wasu maza masu ɗauke da makamai sun kutsa cikin garin Bagudu da ke ƙaramar hukumar Bagudu, inda suka yi garkuwa da ɗan majalisar jim kaɗan bayan kammala sallar isha’i yana komawa gida.

Ta kuma bayyana cewa an tura ƙungiyar haɗin gwiwa da ta ƙunshi dakarun ’yan sanda na musamman, sojoji da masu gadin gari domin gudanar da aikin ceto a yankin.

Labari mai alaƙa: Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar haɗin gwiwar na ci gaba da bincike a hanyoyin da ake zargin ’yan bindigar ke bi da dazukan da ke kewaye domin ceto ɗan majalisar lafiya tare da cafke masu laifin.

Kwamishinan ’yan sanda ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar Kebbi, yana mai bayyana garkuwar da aka yi a matsayin mummunan aiki da ba za a bari ya wuce ba tare da hukunci ba.

Sanarwar ta kuma roƙi jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen aikin tsaro, tana tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here