Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun fatattaki ‘yan bindiga da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Zurmi.
Rundunar ta ce ta kuma kama wata mata mai shekaru 35 da ake zargi da bayar da bayanai ga yan ta’adda watau imfoma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a Gusau.
Abubakar ya ce jami’an ‘yan sandan da ke aiki a Caji Ofis din sun samu sahihan bayanan sirri da ke cewa wasu gungun ‘yan bindiga na shirin kai harin.
Ya ce: “Jami’an ‘yan sanda sun hada kai wuri guda, suka tunkari ‘yan bindigan inda suka yi ta artabu wanda ya dauki tsawon sa’o’i ana musayar wuta.”
“Sakamakon haka, sun kashe daya daga cikin ‘yan bindigar yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji suna zubar da jini a kan hanya saboda raunukan da suka samu.” “Binciken da ‘yan sanda suka yi bayan faruwar lamarin, sun kama wata mata ‘yar shekara 35 da ake zargin imfoma ce daga kauyen Rukudawa.”













































