
An gurfanar da fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Ta Kannywood Amal Umar gaban kotun majistre da ke Gyaɗi-gyaɗi a birnin Kano bisa zargin yunƙurin baiwa ɗan sanda cin hanci.
Ana zargin Amal da yunƙurin ba da cin hancin naira dubu 250 ga wani ɗan sanda mai suna ASP Salisu Bujama da ke rundunar ƴan sandan shiyya ta ɗaya da ke Kano.
A cewar mai gabatar da ƙarar, Amal na yunƙurin bayar da cin hancin ne domin hana binciken ƴan sanda kan zargin saurayinta da almundahanar kuɗi.
Karin labari: Kotu ta umarci NYSC ta bawa mata damar sanya riga da siket
Lamarin ya bayyana ne lokacin da wani Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da ƙorafi ga mataimakin babban spetan ƴan sanda Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama da faɗi da kuɗin da ya kai naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.
Ƙorafin da aka shigar ya sa ƴan sanda gudanar da bincike wanda ya gano cewa saurayin jarumar ya tura mata naira miliyan 13 ta asusun bankinta.
Karin labari: Majalisa ta amince da ƙudurin sabon albashi ga alƙalan Najeriya
A cewar kakakin rundunar ƴan sanda shiyya ta ɗaya, CSP Bashir Muhammed, an gayyaci ƴar fim ɗin domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayin na ta ne ya siya.
Jarumar ta tabbatar da cewa kuɗin da ke cikin asusunta mallakin saurayinta ne duk da ta yi iƙirarin cewa naira miliyan takwas kawai ya tura mata.
Karin labari: Najeriya ta tura sojoji 157 don samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
Bayan da aka ba ta beli ne kuma ta garzaya babbar kotu a Kano domin neman a dakatar da ƴan sanda daga binciken da suke a kanta. Kotun ta hana ci gaba da binciken da ƴan sanda ke yi kan jarumar, abin da ya bawa Amal dama ta yunƙurin ba da toshiyar baki ga ɗan sandan da ke binciken ASP Salisu Bujama.
Jami’in ya yi watsi da cin hancin inda kuma ya kamata ta tare da shaidar zargin ba da cin hancin abin da ya sa aka gurfanar da ita gaban kotun majistre ranar Laraba.
Laifin da ake zargin jarumar ta aikata ya saɓawa sashe na 118 na dokar penal code wanda ta haramta baiwa jami’in ɗan sanda cin hanci.