Yan bindiga sun sace budurwa a Kano bayan karɓar miliyan takwas daga danginta

bandits
bandits

 

‘Yan bindiga sun kai farmaki Garo a Karamar Hukumar Kabo, Jihar Kano, inda suka sace wata budurwa duk da karɓar Naira miliyan takwas daga danginta.

Majiyoyi sun ce maharan, su goma, sun kutsa gidan wani attajiri, Alhaji Auwal, da misalin ƙarfe 1:20 na dare, inda suka tsoratar da iyalinsa kuma suka tara su a wuri guda.

Duk da an basu kuɗin da suka nema, sun yi awon gaba da ‘yar gidan, wacce ta kammala makarantar sakandare.

Har yanzu ba a ji daga gare su ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.

Kakakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana bincike don cafke maharan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here