‘Yan ƙasa da shekaru 18 kawai za’a bawa takardar Haihuwa – NPC

Hukumar, NPC, takardar, haihuwa
Hukumar kidaya ta kasa NPC ta ce ba za'a bawa wadanda suka wuce shekaru 18 takardar haihuwa ba. Daraktan NPC na jihar Oyo Mista Akin Oyetunde ya shaidawa NAN...

Hukumar kidaya ta kasa NPC ta ce ba za’a bawa wadanda suka wuce shekaru 18 takardar haihuwa ba.

Daraktan NPC na jihar Oyo Mista Akin Oyetunde ya shaidawa NAN a ranar Talata a Ibadan, cewa hakan ya kasance ne bisa ga dokar Haihuwa da Mutuwa ta 1992.

Ya ce “NPC tana bin dokar da aka yadda a 1992, don haka duk yaron da aka haifa kafin 1992 ba za’a ba shi takardar haihuwa ba.

Karanta wannan: Kano: Shugaban Karamar Hukuma yayi murabus

“Maimakon shaidar haihuwa mutanen da aka haifa kafin 1992 da wadanda suka haura shekaru 18 za’a ba su shaidar Haihuwa.

“Duk da haka, wadanda basu kai shekaru 18 ba hukumar za ta ba su takardar shaidar haihuwa.”

Daraktan na jihar Oyo ya kara da cewa dukkanin kananan hukumomin jihar suna da cibiyoyin rijistar haihuwa da mutuwa.

Ya bayyana cewa “kowace karamar hukuma tana da nata wuraren rajistar haihuwa da mutuwa. Babu karamar hukumar da take da kasa ko fiye da cibiyoyin rajista uku.

Karanta wannan: Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa Auwal Shu’aibu Aranposu ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.

“Takaddun shaida da aka bayar a cibiyoyin iri ɗaya ne a ko’ina kuma ana yarda da su a duk inda aka ba da su.”

Dangane da kidayar yawan jama’a da gidaje da aka dage tun farko da aka shirya yi a shekarar 2023, Oyetunde ya ce an shirya komai na shirin.

Ya ce “Mun shirya kuma muna bukatar Gwamnatin Tarayya kawai ta ba da dama. Duk kayan aikin motsa jiki sun kasance tuni aka rabawa kananan hukumomi.

“Duk wadanda za su shiga cikin kidayar, an horar da su duk an shirya za su kai ga nasara.”

kamar yadda NAN ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here