Yadda ma’aikatan bankuna ke taimaka wa masu sace kuɗin Kwastomomi- EFCC

IMG 20240824 WA0004

Shugaban Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, Ola Olukoyede, ya ce ma’aikatan banki na hada baki da ‘yan masu kutse ta Internet tare da taimaka wa mazambatan wajen kwashe wa mutane kudi.

Da yake wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, Olukoyede ya ce, masu kutse sun kai wa bankuna shida hare-hare ta Internet.

Shugaban na EFCC ya yi ikirarin cewa ma’aikatan bankin na ba da damar shiga cikin kundin bayanan banki inda masu kutse suka saba yin amfani da su daga kowane bangare na duniya da suke zaune.

Olukoyede ya ce hukumar su ta yaki da cin hanci da rashawa ta kwato Naira biliyan  da miliyan 700, da kuma, wasu biliyan 6 da miliyan 700 da kuma Naira biliyan 3 da miliyan 700 da aka sace a wasu bankunan Najeriya.

Ya jaddada cewa, bisa la’akari da shari’o’in da EFCC ke yi, ana samun sabani a fannin bankunan ne daga jami’ansu da suka fahimci ‘yan banki wadanda suka tsarin.

Shugaban na EFCC, ya kuma ce, “A duk inda sauran mutane suke, ko da a wajen Najeriya ne, za su iya sarrafa tsarin bankin, yanzu mutum na iya kwashe kudi a cikin dakika daya, za su iya kwashe biliyoyin kudi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here