Ɗan jarida kuma mai fafutuka, Agba Jalingo, ya bayyana gidan yari a Najeriya a matsayin mafaka ta cin hanci da rashawa, inda fursunoni ke samun damar yin komai idan suna da kuɗi, kama daga shan miyagun ƙwayoyi har zuwa lalata.
A cikin wata tattaunawa da aka yi a shirin Perspectives na gidan talabijin na Arise, Jalingo ya ce babu wani gidan ajiye masu laifi a Najeriya da ba a biya kuɗi ba.
Ya ƙara da cewa: “Fursunoni masu kuɗi suna rayuwa cikin jin daɗi a cikin kurkuku; suna da waya, ƙwayoyi, da komai da suke so.
Abin kaɗai da ban gani a ciki ba shi ne sassan jiki da bindigogi.
Jalingo ya kuma bayyana cewa akwai wuri na musamman da ake tanadarwa ga waɗanda suka biya cin hanci domin samun sauƙin rayuwa, yayin da marasa ƙarfi ke cunkushewa a cikin ɗakunan da suka wuce ƙima.
Ya danganta wannan matsala da tsananin cin zarafi daga jami’an ‘yan sanda, inda ya bayyana yadda ake amfani da su a matsayin mayaƙan masu kuɗi don tsoratar da ‘yan jarida.
Ya tuna irin azabar da ya sha lokacin da aka tsare shi bisa ƙage na ta’addanci da cin amanar ƙasa, kafin daga bisani a wanke shi daga zargi.
Shi da Azuka Ogujiuba, wata ‘yar jarida da ita ma aka tsare tsawon kwanaki uku a Abuja, sun caccaki Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ), suna zargin shugabanninta da zama masu goyon bayan gwamnati maimakon kare ‘yan jarida daga zalunci.
Dukkaninsu sun jaddada cewa dokokin batanci da kuma Cybercrime Act ya kamata a soke su, domin ana amfani da su ne kawai don toshe bakin masu sukar gwamnati da kuma danniya kan ‘yan jarida













































