‘Yan bindiga sun yi awon gaba da Ango da Amarya a Jihar Zamfara

'yan bindiga, awon, jihar, zamfara
'Yan bindiga a jihar Zamfara sun yi awon gaba da mutum hudu ciki harda ango da amaryarsa a harin da suka kai da tsakar dare a kauyen Madabanciya da ke karama...

‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun yi awon gaba da mutum hudu ciki harda ango da amaryarsa a harin da suka kai da tsakar dare a kauyen Madabanciya da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewa ‘yan bindigar sun kwashe dabbobi da dukiyar jama’a da dama, tare da tilastawa mutanen kauyen kwana a cikin daji don tsoron sake kai masu hari.

“Irin sha biyu saura kwata na dare ‘yan fashi suka fado mana suka daukar mana mutum hudu, suka kwashi dukiya.”

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya ta sake bayar da Ministan Tsaro

‘Yan fashin dajin sun kuma sace kayan dakin amaryar da tufafinta kuma sun ci karensu babu babbaka saboda rashin jami’an tsaro a cewar mazaunin.

“Wannan shi ne karon farko da ‘yan fashin dajin suka shiga wannan yanki kuma a kasa suka shigo.

“Ban san inda suka ajiye abin hawan su ba, kuma suna da yawa sosai rike da makamin nan da ake kira AK, suna ta harbata,”in ji ganau ɗin.

Karanta wannan: Sunayen Yan Najeriya 40 Da Suka Mallaki Jiragen Sama

Mazaunin yankin ya yi ikirarin cewa ‘yan sa kai da ke wani yankin da ke makwaftaka da su ne, su ka kai mu su dauki.

“Akwai wani yanki a kudancin Madabanciya da suke da ‘yan sa kai, da suka ji labari sun kawo dauki amma sun riga sun fita lokacin da suka taho.”

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta ce ba ta da masaniya game da faruwar al’amarin.

ASP Yazid Abubakar wanda shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa rashin samun bayyanai na cikin abubuwan da ke kawo mu su cikas a aikinsu. Shiyasa ba sa iya kai dauki a kan lokaci a cewarsa.

Karanta wannan: Sojoji sun kama fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Harinde

“Taimakon da muke so da ga wurin jama’a, in an samu bayyanai irin wannan a sanar da mu da wuri. Ba sai abu ya riga ya faru a ba mu labari ba.”

Duk da cewa mahukuntan Najeriya na ci gaba da jaddada anniyarsu na kawo karshen matsalar ‘yan fashin daji a yankin arewa maso yammacin kasar, kawo yanzu mazauna wasu yankunan jihohi da matsalar ta yi kamari na ci gaba da fuskantar barazana daga wurin ‘yan fashin dajin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here