Rahotanni daga ƙauyen Yan Kwada da ke yankin Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace mata masu shayarwa huɗu a wani hari da suka kai.
Shugaban kwamitin tsaron yankin Faruruwa da kewaye, Yahaya Bagobiri, ya bayyana cewa ‘yan bindigar da suka iso kauyen a kan babura sun fara da sace mata biyar, sai dai ɗaya ta tsere daga hannunsu.
Bayan sace matan, ‘yan bindigar sun jefar da jariran da suke shayarwa a ƙasa, suka tafi da matan zuwa daji, tare da yin awon gaba da shanu 50 da wasu dabbobi marasa adadi.
Karin labari: Ƴan bindiga sun ƙara tsananta kai hare-hare da garkuwa da mutane a wasu yankunan Kano duk da kasancewar jami’an tsaro
Bagobiri ya bayyana cewa duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da kai hare-hare a kullum, inda a daren jiya suka dawo suka yi barna tare da sace matan masu shayarwa.
Ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar kafin ta ƙara ta’azzara.
A makonnin baya, sojoji sun yi artabu da ‘yan bindiga a yankin, inda aka kashe su goma sha tara yayin da jami’ai biyu daga cikin sojojin suka rasa rayukansu.













































