Yaƙin Gabas ta tsakiya: Gwamnatin Tarayya ta fitar da lambobin gaggawa ga ‘yan Najeriya da ke kasashen waje

Abike Dabiri 506x430

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta kasa ta fitar da lambobin waya na gaggawa domin ‘yan Najeriya da ke cikin matsala a yankin Gabas ta tsakiya.

Matakin ya biyo bayan tashin hankalin da ake samu a yankin gabas ta tsakiya sakamakon yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a, ta bukaci ‘yan Najeriya da ke zaune ko kuma ke wucewa ta yankin da su adana lambobin tare da tuntubar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa da su idan wani lamari na gaggawa ya taso.

Hukumar ta bayyana cewa an tanadi lambobin ne domin samar da taimakon gaggawa na ofishin jakadanci ga ‘yan Najeriya da ka iya bukatar agaji sakamakon yadda al’amuran tsaro ke kara tabarbarewa.

Lambobin gaggawa da aka fitar sun hada da ofishin jakadancin Najeriya da ke Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa: +971 56 884 4130, ofishin karamin jakadancin Najeriya da ke Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa: +971 56 377 8678, ofishin jakadancin Najeriya da ke Kuwait wanda ke kula da Bahrain: +965 97895737, +965 99509288, ofishin jakadancin Najeriya da ke Tel Aviv a Isra’ila: +972 547115279, +234 7064263944, da kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke Doha a Qatar: +974 30197102, +974 30197261.

Sauran sun hada da ofishin jakadancin Najeriya da ke Beirut a Lebanon: +961 78 861 779, +234 8038954425.

Haka kuma akwai ofishin jakadancin Najeriya da ke Riyadh a Saudi Arabia wanda ke kula da Oman: +966 542149456, +966 565695763, ofishin karamin jakadancin Najeriya da ke Jeddah: +966 560965633, da kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke Amman a Jordan wanda ke kula da Iraq: +962 777369428, +962 776594020.

Hukumar ta sake jaddada cewa ya kamata ‘yan Najeriya da ke kasashen waje su kasance cikin taka tsantsan, su bi shawarwarin tsaro na kasashen da suke ciki tare da ci gaba da tuntubar ofisoshin jakadancin Najeriya domin samun bayanai da taimako.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here