Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa kwace filin na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata na 13 ga Maris 2025, wadda ta samu sa hannun shugaban sashen kula da filaye na babban birnin ƙasar, Chijioke Nwankwoeze.
Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk kuwa da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen.
Rahotanni dai na cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da ministan ya ƙwace a Abuja.