Wasu ƴan asalin Kano 2 sun mutu a ramin hakar ma’adinai a Neja

Mining pit collapsed new 750x430

Rundunar ‘yan sanda a Neja ta tabbatar da mutuwar mutane biyu bayan ruftawar wani ramin hakar ma’adinai a yankin Farin-Doki da ke karamar hukumar Shiroro.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da hakan a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna.

Abiodun ya ce ramin ya rufta ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya rufe wasu ma’aikatan hakar ma’adinai guda biyu da aka bayyana sunayensu da Buhari Kano da kuma Malam Tasiu dukkansu daga jihar Kano.

A cewarsa, jami’an ‘yan sanda daga reshen Erena da mazauna yankin sun yi gaggawar zuwa wurin inda suka fara aikin ceto.

Karanta: Naira miliyan 300 da jihar Rivers ta ba mu kyauta ne, ba kudin karbar bakuncin taro ba – NBA ta yi martani ga Ibas

Abin bakin ciki, an samu wadanda abin ya shafa ba su da rai, kuma an kai gawarwakinsu asibitin Zumba domin ci gaba da bincike.

Bincike na farko ya nuna cewa wadanda abin ya shafa na hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a wurin cikin dare.

Abiodun ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here