Wasanni:Kano Pillars Ta Sayi Sabbin ‘Yan Wasa Goma Sha Ɗaya

kano pillars 1
kano pillars 1

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars dake buga gasar pirimiyar Najeriya (NPFL), ta sayi sabbin ‘yan wasa 11 kafin kakar wasannin 2021/2022, a cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Lahadi, a Kano.

Jami’in watsa labarai na kungiyar Idris Malikawa, ya ce bayan gudanar da taron kulob din a ranar Asabar, sun amince da yi wa ‘yan wasa 32 rajista a kakar wasa mai zuwa, da suka hada da wadanda aka rike da sabbin’ yan wasa.

Sabbin ‘yan wasan da aka sanyawa hannu su ne: Saidu Salisu daga Akwa United, Gabriel Jeremiah, Ugochukwu Nwachukwu daga Cyprus, Isma’il Nasir daga Nasarawa United, Mark Daniel daga Warri Wolves, da Yusha’u Garba daga Katsina United.

Karanta Wannan: Buhari Ya Tafi Taron Majalisar Dinkin Duniya na 76 a Amurka

Sauran sune; Isah Usman daga kungiyar kwallon kafa ta Rarara, Taro Oluwaseun daga Smart City, Usman Maidubji daga Plateau United, Wisdom Ikechi daga Bayelsa United, Muhsin Attahiru daga Sokoto United.

Malikawa ya ce, mahukuntan kulob din suna kuma tattaunawa kan cinikin Emeka Onyema daga Nasarawa United da Madaki Dauda daga Enugu Rangers.

Jami’in watsa labaran ya yi bayanin cewa an yi wa ‘yan wasan gaba guda biyar – Sulaiman Ibrahim, Haruna Musa, Abdullahi Ahmed, Shamsuddeen Abdullah, da Shehu Muhammad karin girma daga karamar kungiyar.

Malikawa ya kuma sanar da cewa, kulob din ya rike ‘yan wasa 18 tare da yi wasu 32 rajista a kakar wasa mai zuwa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here