Wahala ta saka ni kasuwancin gawayi – ɗalibin jami’ar Ahmadu Bello

Charcoal new

Wani ɗalibi a jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Joshua Christopher, ya bayyana cewa matsin tattalin arziki ne ya tilasta masa shiga sana’ar gawayi, wadda yanzu ta zama hanyar samun kuɗin rayuwa yayin da yake ci gaba da karatunsa.

Christopher ya bayyana haka ne yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a lokacin da suka kai ziyarar karatu a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda ya ce ya fara sana’ar ne domin taimaka wa kansa a gida da kuma a jami’a, duk da saninsa cewa tana da illa ga muhalli.

Ya ce aikin gawayi yana farawa ne da sare itatuwa, a yankasu, a jera su, a rufe da ƙasa, sannan a ƙone su cikin yanayin zafi da ake sarrafawa.

Ya bayyana cewa tsarin na iya ɗaukar kwanaki huɗu kafin a gama, kuma wani zagaye na iya samar da buhuna shida na gawayi.

Christopher ya amince cewa sare itatuwa na kawo illa ga muhalli, amma matsin tattalin arziki ya jefa matasa da dama cikin wannan sana’a, har ma yace idan mutum zai sare itace ɗaya, to ya kamata ya dasa biyu ko uku domin maye gurbinta.

Haka kuma, wani ɗan kasuwar gawayi mai suna Frank Bala, ɗan shekara 25, ya bayyana cewa ya kwashe shekaru uku yana cikin kasuwancin kuma yana samun ɗan riba mai kyau.

A cewar sa, wasu lokuta sukan sayar da buhuna 50 a rana, sai dai farashin na sauyawa bisa yanayi.

Bala, wanda ya kammala karatu a fannin noma, ya ce duk da saninsa kan illa ta sare itatuwa, wannan kasuwanci na zama mafita ga matasan da ba su da aiki.

Ya ce mafi yawan masu sana’ar suna fuskantar matsalolin tsaro amma suna daidaita da jami’an da ke lura da dazuka idan sun zo dubawa.

Ya roƙi gwamnati da kungiyoyin ci gaba su samar da hanyoyin neman abin yi na halas ga matasa domin rage sare itatuwa da kare muhalli.

A nasa bangare, ma’aikatar muhalli ta jihar Kaduna ta ƙara ƙaimi wajen kare dazuka ta hanyar tura masu gadin daji da haɗin gwiwa da jami’an tsaro don dakile sare itatuwa da yin gawayi ba bisa ƙa’ida ba.

Mataimakin daraktan kula da albarkatun daji, Godwin Michael, ya ce gwamnati tana tsayawa wajen aiwatar da dokar hana sare itatuwa da inganta kula da dazuka.

Ya tunatar da cewa tun a shekarar 2015, gwamnatin jihar ta ayyana dokar ta baci kan dazuka bayan gano cewa murhun daji na Kaduna ya faɗi ƙasa da kaso 15 cikin ɗari, ƙasa da abin da ƙa’ida ta duniya ta shimfiɗa na kaso 25.

Ya ce ma’aikatar na aiki da jami’an ‘yan sanda wajen kafa wuraren bincike don tabbatar da bin doka.

Ya ƙara da cewa kusan kashi 90 cikin ɗari na gawayin da ke shiga Kaduna daga jihohin Nasarawa, Neja, da Kogi yake zuwa.

Haka kuma, jami’in kula da dazuka na Kajuru, Zakariya Naye, ya bayyana cewa rashin kayan aiki da abin hawa na daga cikin manyan matsalolin da suke fuskanta wajen dakile masu sare dazuka ba bisa ƙa’ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa ziyarar da aka kai ta karkashin ƙungiyar “cike gibin fata ga yankin Afirka (BTG) Bridge That Gap Hope for Africa Initiative (BTG), na shirin ƙarfafa mata da juriya kan sauyin yanayi, wanda ke ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa na PACE da ofishin ci gaban ƙasashen Birtaniya ke tallafawa.

An kuma gudanar da taron kwana uku na horas da ‘yan jarida kan yadda za su inganta rahotanni masu nasaba da sauyin yanayi, inda masana muhalli suka jaddada illar sare itatuwa da tasirinta wajen haifar da iskar gas mai dumama duniya.

 

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here