UNGA80: Gwamna Yusuf ya tabbatar da ci gaba da shirin ciyar da ɗalibai da kuma janyo masu zuba hannun jari daga waje

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430 (1)

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na jawo hadin gwiwar kasa da kasa domin bunkasa ilimi, kiwon lafiya da cigaban tattalin arziki a jihar.

Yusuf ya bayyana hakan ne kan sakamakon halartar Kano a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA80) da aka gudanar a New York, inda ya sanar da sabbin damar shirin ciyar da ɗalibai, tallafin kiwon lafiya da kuma jarin waje.

Gwamnan ya bayyana cewa Sarkin Kano, Khalifah Muhammadu Sanusi II, tare da Darakta-Janar na hukumar bunkasa jarin Kano (Kan-Invest), Muhammad Naziru Halliru, ne suka wakilci jihar a babban taron.

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a gefen taron UNGA80, Sarkin Kano ya gana da ‘yar kasuwa daga Kenya, Wawira Njiru, shugabar kamfanin Food4Education, domin tattaunawa kan hadin gwiwar shirin ciyar da ɗalibai a Kano, ciki har da samun damar shiga tallafin da bankin raya Afirka (AfDB) ya ware domin irin wannan shiri.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa gwamna Yusuf ya ce wadannan tarurruka sun nuna aniyar gwamnatinsa wajen sanya Kano a sahun gaba a matsayin cibiyar jarin Najeriya. Ya kara da cewa za a gabatar da tsarin jarin shekaru biyar domin jawo masu zuba jari, kara kudaden shiga da kuma fadada damammaki ga al’ummar Kano.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here