UNGA: Ƙasashen Birtaniya, Ostireliya da Kanada sun amince da ƙasar Falasdinu

682090 750x430

Ƙasashen Birtaniya, Ostireliya da Kanada sun sanar a ranar Lahadi cewa sun amince da kafuwar ƙasar Falasdinu, wani muhimmin sauyi a siyasar ƙasashen yammacin duniya, lamarin da ya tayar da fushin Isra’ila nan take.

Haka kuma, Portugal ta bayyana cewa za ta biyo baya wajen bayyana irin wannan matsayi a ranar, yayin da Isra’ila ke ƙarƙashin matsanancin matsin lamba daga ƙasashen duniya saboda yaƙin Gaza da ya fara bayan harin Hamas na 7 ga Oktoba, 2023.

Fira Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana a shafinsa na X cewa an ɗauki wannan mataki ne “don farfaɗo da fata ga zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ilawa, da kuma aiwatar da mafita ta ƙasashe biyu.”

Wannan ya sa Birtaniya da Kanada suka zama ƙasashe na farko daga cikin G7 da suka ɗauki irin wannan mataki, yayinda ake sa ran Faransa da sauran ƙasashe za su biyo baya a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) da zai fara a New York ranar Litinin.

Fira Ministan Kanada, Mark Carney, ya rubuta a shafinsa na X cewa: “Kanada ta amince da ƙasar Falasdinu, kuma muna bayar da haɗin kai wajen gina makomar zaman lafiya ga Falasdinu da Isra’ila.”

Wannan matakin ya sanya ƙasashen su sabawa da ra’ayin Amurka da Isra’ila, inda Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kiran kafa Falasdinu zai “ƙalubalanci wanzuwar Isra’ila” kuma ya zama “lada ga ta’addanci.”

Tun bayan harin Hamas, Isra’ila ta ƙara tsananta hare-haren ta a Gaza, inda aka samu lalacewar gine-gine, mutuwar mutane fiye da dubu 65 bisa ga ma’aikatar lafiya ta Gaza, yawanci fararen hula, abin da ya haddasa mummunar rikicin jin ƙai.

Wannan ya janyo ƙarin goyon bayan jama’a a ƙasashen yamma, musamman a Birtaniya inda rahoton YouGov ya nuna kashi biyu bisa uku na matasa suna goyon bayan kafuwar Falasdinu.

Shugaban Falasdinu, Varsen Aghabekian Shahin, ya ce amincewar ba alama ba ce kawai, domin tana aika sako kai tsaye ga Isra’ila cewa ba za ta iya ci gaba da mamayewa har abada ba.

Portugal ma ta bayyana a New York cewa ta yanke hukuncin amincewa da Falasdinu, inda Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa ya ce hakan zai “ci gaba da rike fata na kafuwar ƙasashe biyu.”

Tun sama da ƙarni guda, Birtaniya ta taka rawa wajen kafa harsashin kafuwar Isra’ila ta hanyar sanarwar Balfour ta 1917.

Yanzu kuwa, sama da ƙasashe 140 daga cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 ne suka riga suka amince da ƙasar Falasdinu.

Wannan sabon matsayi daga manyan ƙasashen yamma na nuni da cewa akwai ƙara canji a siyasar duniya kan rikicin Falasdinu da Isra’ila.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here