Kabiru Tanimu Turaki daga jihar Kebbi ya zama shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a babban taron zaben shugabannin jam’iyyar na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Ibadan a ranar Asabar.
Turai ya samu kuri’u 1,516 inda ya kayar da abokin takararsa Garba Lado, wanda ya samu kuri’u 41 kacal a sakamakon kada kuri’un da aka kammala.
Sakataren kwamitin shirya babban taron zaben, Sanata Ben Obi, ne ya sanar da sakamakon bayan kammala kirga kuri’un da aka jefa a wurin taron.
Obi ya bayyana cewa wakilai 3,141 ne suka halarta, inda aka tantance 2,745, sannan wasu kuri’u 275 aka bayyana su a matsayin wadanda ba su da inganci.
Haka kuma ya bayyana cewa Solarin Adekunle ya fito a matsayin mataimakin sakataren shirya harkokin jam’iyya na ƙasa, yayin da aka ce an tsayar da mutane 17 takara ba tare da hamayya ba.
Kamfanin dukkanin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, Turaki ya taɓa zama minista a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.












































