Tsohon shugaban hukumar NYSC da aka yi garkuwa da shi ya shaƙi iskar ‘yanci

tsiga

Birgediya-Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ya shaki iskar ‘yancin bayan ya shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) daga mahaifarsa da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025 tare da wasu mazauna garin guda tara.

Sai dai bayan an biya su kudin fansa daga iyalansa, wanda har yanzu Akwai alkaluma masu karo da juna dangane da kudin da aka biya.

Yayin da wasu ke ikirarin cewa an biya Naira miliyan 60 DailyTrus ta samu tabbacin cewa ainihin kudin da aka biya na sakin sa ya haura haka har sau uku.

Labari mai alaƙa: Wadanda suka sace tsohon shugaban NYSC sun bukaci Naira miliyan 250 kudin fansa

Wani makusanci a danginsa ya shaida wa wakilinmu cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye shu har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan, inda suka sanya Janar din a waya domin tattaunawa da su.

“An kai musu kudin, kuma sai bayan mako daya, wato ranar Talata 11 ga watan Maris, sai suka kira muka ji muryarsa,” inji majiyar.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun yi waya suna neman a kara musu kudi, wanda ya ce ba a ba su ba.

“Babu wani abu da aka kara a zahiri, kuma a yayin da muke magana, suna jihar Zamfara inda za su kai Janar din zuwa Abuja,” inji majiyar.

Wata majiya mai karfi ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga ga DailyTrust l, yayin daajiyoyi na kusa a danginsa suka ce yana cikin koshin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here