Tsoffin gwamnonin Zamfara huɗu sun gana kan matsalar tsaron jihar

Gwamnonin, Zamfara, matsalar, tsaro
Tsofaffin gwamnonin jihar Zamfara huɗu sun yi wata ganarwar sirri domin tattauna yadda za'a magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.Cikin wata sanarwa da...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Tsofaffin gwamnonin jihar Zamfara huɗu sun yi wata ganarwar sirri domin tattauna yadda za’a magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar ya ce tsofaffin gwamnonin jihar da suka haɗa Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da kuma ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Mohammed Matawalle sun gana ne a ranar Asabar da daddare.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta sake nanata dokar haƙar yashi da ma’adanai ba bisa ka’ida ba

‘”Tsoffin gwamnonin da suka gana a gidan ministan tsaron sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa kan batutuwan da suka shafi matsalar tsaron jihar da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar, don inganta ci gaban rayuwar al’ummar jihar ta fannonin ilimi da na lafiya” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnonin na cewa idan ana batun tsaro, ya kamata a ajiye duk wani bambanci musamman na siyasa da ke tsakani domin samawa al’umma mafita.

A baya-bayan nan dai jihar Zamfara na fama da ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da ke sace mutane domin neman kudin fansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here