Kungiyar tsoffin ’yan sanda masu ritaya da ke ƙarƙashin tsarin biyan Fansho na tarayya da ake tara kuɗi (CPS) ta sanar da shirin gudanar da abin da ta kira “Babbar zanga-zangar lumana” a gaban majalisar dokokin ƙasa a ranar Litinin mai zuwa.
A watan Yulin da ya gabata, tsoffin ’yan sanda sun gudanar da irin wannan zanga-zanga a Abuja inda suka buƙaci a cire su daga tsarin tara kuɗin fansho da suke kiran zalunci.
A lokacin, sun yi tattaki daga hedikwatar rundunar ’yan sanda zuwa majalisar dokoki, suna rera wakokin gwagwarmaya tare da riƙe kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce irin su “Shekaru 35 na aiki, Naira miliyan 3 fansho? Abin kunya!” da kuma “Muna buƙatar hukumar fanshon ’yan sanda yanzu!”
Cif Sufeto Mannir Lawal Zariya (mai ritaya), shugaban reshen Kaduna na ƙungiyar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa mambobin ƙungiyar na fama da matsananciyar talauci, rashin samun kulawar lafiya, da ma rasa ikon biyan buƙatun abinci na yau da kullum.
Ya ce akwai ma waɗanda suka janye ’ya’yansu daga makarantu sakamakon tsadar rayuwa, har ma da yawaitar mace-macen tsoffin jami’an.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wakilai daga jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya za su haɗu a majalisar dokoki domin ci gaba da wannan koke.
Wannan mataki ya biyo bayan taron ta Internet da suka gudanar a ranar 22 ga Satumba, inda suka sake jaddada buƙatar ficewar ’yan sanda daga tsarin tarin kuɗin fansho.
Karanta: Gwamnati ta gargadi jama’a kan tallan bogi da aka kirkira da AI da sunan Shugaba Tinubu
Cif Sufeto Lawal ya tuna cewa shekaru fiye da 15 kenan suna kai korafi da rubuta takardu ga gwamnati da majalisar dokoki, har ma da gudanar da zaman sauraron jama’a guda uku.
A duk lokacin da suka gabatar da hujjoji, sun nuna yadda fanshon da suke samu ya yi ƙasa ƙwarai idan aka kwatanta da na sojoji da jami’an hukumar tsaron Cikin Gida, duk da haka, bai kawo wani sauyi mai ma’ana ba.
Ya bayyana cewa majalisar dokoki ta tara ta amince da kudirin cire ’yan sanda daga tsarin tarin kuɗin fansho, amma ya tsaya cak bayan kasa daidaita shi da na majalisar dattawa.
Duk da alkawarin da aka yi musu a watan Yuli, Cif Sufeto Lawal ya zargi Hukumar Kula da Fansho da ƙoƙarin dakile ficewar, inda ta gabatar da wasu tayin ƙarin kuɗin alawus da inshorar lafiya domin su ci gaba da kasancewa a tsarin.
Sai dai ƙungiyar ta yi watsi da tayin, tana mai dagewa kan cikakken ficewa zuwa tsarin tsohon fansho (DBS), tare da kafa hukumar fansho ta ’yan sanda.
Cif Sufeto Lawal ya ce dukkan mambobi daga shiyyoyi shida na ƙasar sun yi watsi da shirin Hukumar Fansho tare da jaddada buƙatarsu ta kafa hukumar ta musamman.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa zanga-zangar da aka tsara a gaban majalisar dokoki za ta gudana kamar yadda aka shirya, tare da kira ga dukkan tsoffin jami’ai a fadin ƙasa da su halarta domin ganin an cimma wannan buri.













































