Tsofaffin Sojoji sun soki Wike kan rikicinsa da jami’in Sojan ruwa, sun buƙaci ya bada haƙuri

WhatsApp Image 2025 11 11 at 2.25.36 PM 1 750x430

Tsofaffin sojojin Najeriya sun yi Allah-wadai da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, bisa rikicinsa da wani jami’in sojan ruwa yayin wani rangadin aiwatar da doka a filin da ake takaddama a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin ƙungiyar haɗin gwiwar tsofaffin sojoji, Abiodun Durowaiye-Herberts, ya fitar ta soki Wike saboda amfani da kalmomin raini ga jami’in a bainar jama’a lokacin da suka yi sa-in-sa.

A cewar tsofaffin sojojin, bai dace ba a matsayin wani mai rike da mukamin gwamnati ya zagi jami’in tsaro da yake gudanar da aikinsa na hukuma.

Sun bayyana cewa jami’in da ke cikin kayan soja na wakiltar ikon daular Najeriya, kuma raina irin wannan jami’i yana lalata martabar hukumomin gwamnati.

Kungiyar ta yi gargaɗi ga duk wanda zai nemi a ɗauki matakin ladabtarwa kan jami’in da lamarin ya shafa, inda ta ce za su gudanar da zanga-zanga a ofishin da kuma gidan ministan babban birnin tarayya idan hakan ta faru.

Tsofaffin sojojin sun kuma jaddada cewa jami’an tsaro suna rantsuwar biyayya ga ƙasa ba ga mutum ɗaya ba, don haka suka bukaci Wike ya nemi afuwa kan maganganun da ya yi.

Sun ce abin da Wike ya aikata ya rage kimar kujerar minista, kuma ya kamata ya nemi afuwa saboda yin amfani da kalmomin ɓatanci da ba su dace ba ga jami’in tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here