Tsaro: Gwamnan Kano ya ziyarci sansanin ƙungiyar tsaro ta JTF a Kano, ya yi alkawarin ci gaba da bada tallafi

IMG 20251202 WA0083 750x430

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai ziyarar aiki zuwa sansanin aikin ƙungiyar haɗin guiwa ta tsaro ta JTF da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a ranar Talata, inda ya tabbatar wa jami’an tsaron cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ba su goyon baya wajen tinkarar barazanar tsaro da ta taso a yankin.

Ziyarar ta gwamnan ta mayar da hankali ne wajen duba halin tsaro, ƙarfafa jami’an tsaron, da kuma inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da gwamnatin jihar domin samun nasarar kare al’umma daga ayyukan ta’addatawa.

Gwamnan ya tabbatar wa jami’an tsaron cewa gwamnatinsa za ta dage wajen kula da jin daɗin su tare da samar da duk wasu kayan aiki da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya dace, musamman wajen magance aikata laifuka da ke kuntata rayuwar jama’a.

Ya bayyana cewa matsalolin garkuwa da mutane da fashi da makami da aka samu a wasu sassan Tsanyawa da Shanono sabbin abubuwa ne a jihar, kana ya nuna kwarin gwiwar cewa ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu za su dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Gwamna Yusuf ya yaba da jajircewar jami’an tsaron, tare da tabbatar wa al’ummar yankin cewa mutanen da aka yi garkuwa da su za a ceto su cikin koshin lafiya, sannan gwamnati za ta samar da sabon ofishin tsaro domin tsare yankin daga ƙarin barazana.

Shugaban rundunar sojojin Najeriya na bataliya ta 3, Birgediya Janar Ahmed Tukur, ya bayyana cewa ƙungiyar haɗin guiwar ta ƙunshi dakarun sojoji, rundunar sojin sama, ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, hukumar tsaro ta Civil Depence, da ƙungiyoyin sa kai, kuma suna gudanar da aikin yau da kullum a wuraren da ake ganin suna da rauni a yankin.

A yayin ziyarar, gwamnan ya duba kauyen Yankamaye inda aka yi garkuwa da mutane shida tare da kashe wata tsohuwa.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here