Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi a safiyar Laraba

Tinub, jawabi, najeriya, ranar, dumokuradiyya, ci gaba, sauye-sauyen, tattalin arziƙi, wahalhalun, fuskanta
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasar jawabi a wani ɓangare na Ranar Dimokuraɗiyya a gobe Laraba.

Wata sanarwa da fadar sugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe, tana mai shawartar dukkan gidajen rediyo da talabijin su ɗauki jawabin daga gidan talabijin na ƙasa NTA da kuma gidan rediyon tarayya na FRCN.

Ana sa ran shugaban zai yi magana kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekara ɗaya da hawa mulki bayan rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Karin labari: Rikicin Masarautar Kano: Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci Hakimai su shirya hawan Sallah Babba

Kazalika, ana sa ran zai taɓo batun mafi ƙarancin albashi da ake ta taƙaddama a kai tsakanin gwamnatinsa da kuma gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago, abin da har ya jawo yajin aiki na kwana ɗaya.

Babu tabbas ko shugaban zai sanar da sabon mafi ƙarancin albashin bayan Naira Dubu 62,000 da gwamnati ta sanar a wannan makon, wanda kuma ƙungiyoyin NLC da TUC suka yi watsi da shi kuma suke neman Naira Dubu 250,000.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here