Tinubu zai tafi ƙasashe biyu domin ziyarar aiki

Tinubu depart US 750x430

Shugaba Bola Tinubu, zai bar Abuja ranar Asabar 28 ga watan Yuni, domin ziyarar kasashe biyu a Saint Lucia da Brazil.

Ziyarar sa ta farko ita ce Saint Lucia, inda zai kai ziyarar aiki a wani bangare na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa tsakanin Najeriya da kasashen da ke yankin Caribbean da kuma ƙarfafa hadin gwiwa tsakanin ƙasashen.

A ƙarshen ziyarar yankin na Caribbean, shugaba Tinubu zai wuce zuwa ƙasar Brazil domin halartar taron koli na BRICS karo na 17 a Rio de Janeiro.

A ziyarar ta Saint Lucia, shugaba Tinubu zai kai ziyarar ban girma ga Cyril Errol Melchiades Charles da Fira Minista Philip Pierre.

Wani muhimmin lamari a ziyarar shi ne jawabin da Shugaba Tinubu zai yi a taron hadin gwiwa na musamman na mambobin Majalisar dattawa da ta wakilai na Saint Lucia a William Jefferson Clinton Ballroom da Sandals Grande da kuma Gros Islet.

An gayyaci shugabannin gwamnatocin kungiyar kasashen gabashin Caribbean OECS da manyan jami’an gwamnati da jami’an diflomasiyya da mambobin al’ummar Najeriya a kasar da Darakta Janar na OECS Dakta Didacus Jules, don halartar taron na musamman.

Shugaba Tinubu zai gudanar da wani babban taron cin abincin rana tare da shugabannin gwamnatocin da suka kasance mambobi a ƙungiyar ta OECS, bayan taron hadin gwiwa na wakilan majalisar Saint Lucia.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here